Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta ce ta gano na’urorin tantance masu kada kuri’a 21 daga cikin 69 da suka bace a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun dokoki a jihar Bayelsa.

Kwamishinan zaben jihar Monday Udo Tom, ya bayyana haka a wajen taron masu ruwa da tsaki a ofishin hukumar dake Yenagoa babban birnin jihar.

Ya ce a wannan karon ba za a harhada sakamakon zabe a ofishin hukumar dake jihar ba, za a yi ne a shelkwatan hukumar, inda za a fara tun daga jami’an gudanar da zaben a rumfunan kada kuri’a.

Tom ya ce a wannan karon hukumar ta gudanar da tsare-tsare da za su taimaka dan ganin ba a samu matsala da na’urar tantance masu kada kuri’ar ba.