Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce duk da jihar Gombe ta na zaune lafiya a yanzu, kaddamar da sabuwar rundunar tsaro ta ‘Operation Hattara’, matakin kariya ne daga fadawa matsalar tsaro.
Inuwa Yahaya ya bayyana haka ne, yayin bude taron zaman lafiya da samar da tsaro mai dorewa da aka gudanar karo na farko a jihar Gombe.
Taron, wanda ya samu halartar shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Usman Alkali Baba da sauran jagororin tsaro, ya duba hanyoyin dakile matsalolin tsaro na zamani da na habbaka atttalin arziki da zamantakewa.
Gwamna Inuwa, ya ce taron zai bada dama ga jami’an tsaro da na gwamnati da ma sauran masu ruwa da tsaki wajen samar da sabbin dabarun tabbatar da dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Gombe.
Ya ce an dauki matasa 500 a matsayin jami’an tsaro da zirga- zirga da muhalli na jihar Gombe, da zummar tallafa wa hukumomin jihar wajen tabbatar da doka da oda.



































