Gwamnatin Tarayya ta kammala dukkan shirye-shiryen da su ka dace, domin bijiro da sabbin hanyoyin karbar haraji a Nijeriya.

Ministar kudi Zainab Ahmed ta bayyana haka a gaban Kwamitin Kasafi na Majalisun Tarayya, inda ta ce za a bijiro da hanyoyin ne domin sama wa gwamnati kudaden shiga.

Ta ce an karkasa hanyoyin samun kudaden harajin zuwa gida uku, wadanda ta roki Majalisun Tarayya su bada goyon bayan shigo da sabbin hanyoyin karbar haraji daga ‘yan Nijeriya.

Ministar ta cigaba da cewa, gwamnatin tarayya ta dauki tsauraran matakan toshe duk wata kofar da harajin da ya kamata a karba ba ya shiga aljihun gwamnati.Idan dai za a iya tunawa, a makon da ya gabata ne, Ministan Kasafi da Tsare-tsare Udo Udoma, ya ce za a kara yawan harajin jiki-magayi da aka fi sani da ‘VAT’ a Turance, domin a samu kudin da za a rika biyan karin albashin da aka yi wa ma’aikta daga naira 18,000 zuwa naira 30,000.

Leave a Reply