Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta ce ba za ta gudanar da wani sabon zaben gwamna da na ‘yan majalisun dokoki a jihar Rivers ba.
Wannan kuwa, ya biyo bayan ficewar dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar AAC Biokpomabo Awara daga taron masu ruwa da tsaki da hukumar zaben ta shirya, domin ci-gaba da zaben jihar da ta dakatar a ranar 9 ga watan Maris.
Haka kuma, ‘yan takarar gwamnan jihar na jam’iyyun SDP da LP sun fice daga dakin taron da aka gudanar a garin Fatakwal.
Kwamishinan zabe na kasa mai kula da jihohin Bayelsa da Rivers da Edo May Agbamuche-Mbu, ya ce hukumar zaben ba za ta iya gudanar da wani sabon zabe a jihar ba.
Ya ce hukumar za ta dawo da ci-gaba da tattara sakamakon zaben jihar Rivers a ranar 2 ga watan Afrilu, ya na mai cewa, makasudin taron shi ne tunatar da masu ruwa da tsaki a kan shirye-shiryen da hukumar ta yi.
Gwamnan jihar Rivers Nyesom Ezenwo Wike, ya bukaci kada a sanya jami’an tsaro yayin zaben, domin tabbatar da ganin an gudanar da sahihin zabe a cikin kwanciyar hankali.



































