Hukumar mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa EFCC ta yi nasarar kama wasu makudan miliyoyin kudi a babban filin jirgin sama na jihar Borno.

Hukumar EFCC ta ce kudin da ta kama sun kai naira miliyan 54 daga hannun wasu mutane 4 da kuma wasu kungiyoyi 2 masu zaman kan-su da ke aiki a jihar ta Borno.

Hukumar ta ce wadanda ake zargi da mallakar kudadden  sun hada da  Abdullahi Yarima, Francis Bako, Saraya Umaru, da kuma James Yadzugwa.

Hukumar EFCC na ci gaba da gudanar da bincike a kan wannan kudi da aka samu,  da kuma kungiyoyin da ake zargin da hannun su a cikin safarar su.

Kungiyoyin da ake bincike sun hada da Kungiyar Mercy Corps da kuma Development Exchange Centre dake aiki a yankin Arewa maso yamma a dalilin rikicin kungiyar Boko Haram.EFCC ta ce ta gano cewar kungiyar Mercy Corps’ ta na da asusu daban-dabam guda 15 dauke da lambar BVN mabanbanta, yayin da ita kuma Development Exchange Centre take da akalla masu ajiyan kudi 40 dabam-dabam

Leave a Reply