Hukumar Allazan ta kasa ta bayyana cewa, ba ta da izinin tilastawa wata Hukumar Allazan jiha a kan ta bayyana kudin aikin Hajjin shekarar 2019.

Babbar jami’ar watsa labarai ta Hukumar Misis Fatima Usara, ta bayyana hakan ranar Alhamis a garin Abuja.

Usara ta ci gaba da cewa, har yanzu Hukumar ta kasa tare da na jihojin da kuma sauran masu ruwa da tsaki ba su gama tsayar da matsaya a kan kudin aikin Hajjin bana ba.

Hukumar NAHCON tana jawo hankalin maniyyata aikin Hajjin shekarar 2019, da kuma daukacin mutane cewa, ba ta da izinin tursasawa wata Hukumar Allazai a kan ta bayyana kudin aikin Hajjin shekarar 2019.

Usara ta ce, an sanar da fara rijistan aikin Hajjin shekarar 2019, tun a watan Nuwambar shekarar 2018.

Ta kara da cewa, kudin rijistar an kiyasta Naira miliyan 1.5, wanda za a saka a banki tare da zuwa ofishin Hukumar domin amsar takardar shaida.

A cewarta, za a iya biyan kudin duka ko kuma a biya kashi-kashi, sannan sai a garzaya ofishin Hukamar tare da nuna takardar biyan kudi na banki.

Usara ta gargadi maniyyata da su guji biyan kudi ta hannun wakilan Hukumar ko kuma wani jami’inta, biyan kudin ya ta’allaka ne ga banki kadai.

Leave a Reply