Gwamnatin tarayya ta ce ta dauki matakan karawa jami’an soji kwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu, tare da tsaron lafiyar ‘yan kasa a lokacin atisaye na musamman domin tabbatar da zaman lafiya.

Ministan tsaro Mansur Dan Ali, ya ce gwamnatin tarayya ta yi hakan ne ta hanyar sakewa jami’an tsaron tsari kan yadda za su rika gudanar da ayyukansu da atisaye.

Dan Ali ya bayyana hakan ne a lokacin taron ministoci kan tabbatar da zaman lafiya da tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma na majalisar dinkin duniya.  

Ya ce kadan daga cikin matakan da aka dauka shine rashin amincewa da gazawa kowacce iri, tare da kauda duk wasu abubuwa da suka shafi cin zarafi, da girmama na gaba da dai sauran su.

Sannan ya tabbatarwa majalisar da dinkin duniya shirin da Najeriya ke da shi wajen kokarin samar da zaman lafiya da tsaro, ta yadda za a samu ci gaba mai dorewa.

Leave a Reply