Shugabannin jam’iyyar APC, sun fara gaugawan dinke duk wata baraka da ka iya tasowa sakamakon zaben Lawan Ahmad a matsayin shugaban majalisar dattawa.

Shugaba kasa Muhammadu Buhari dai ya gana da daya daga cikin masu neman kujerar shugabancin majalisar dattawa Sanata Danjuma Goje.

Haka kuma, jiga-jigan jam’iyyar APC da zababbun sanatoci sun gana da Danjuma Goje domin tabbatar da cewa jam’iyyar PDP ba ta hure masa kunne ba.

Rahotanni sun nuna cewa, gwamnan jihar Borno Kashim Shettima da magoya bayan Ahmed Lawan sun yi taro da daya daga cikin masu neman kujerar shugabancin majalisa, Sanata Ali Ndume domin lallashin sa ya amince da zabin APC.

A na shi bangaren kuma, Sanata Abdullahi Adamu ya janye muradin sa, ya goyi bayan Ahmed Lawan saboda shugaba Muhammadu Buhari ya yi na’am da takarar sa.

Wata majiya ta ce an gudanar da tarurruka goma sha daya, daga ranar Talata zuwa Laraba domin yin sulhu tsakanin sanatocin APC da ke sha’awar takarar shugabancin majalisar.

Leave a Reply