Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya ce Nijeriya ba ta fatan sake samun yakin basasa kamar yadda ya auku a shekara ta 1967.

El-Rufai ya bayyana haka ne, lokacin da ya ke yi wa masu yi wa kasa hididima da aka tura jihar jawabi yayin kammala zaman su a sansanin horarwa a Kaduna.

Ya ce zai kyautu matasan Nijeriya su nesanta kan su daga duk abin da ka iya zama barazana ga zaman lafiyar kasar nan.

El-Rufa’i, ya kuma gargadi masu yi wa kasa hidimar, wadanda za a yi amfani da su wajen gudanar da aikin zaben shekara ta 2023 kada su bari a yi amfani da su wajen tafka magudi.

Da ya ke jawabin ta bakin mataimakiyar sa Hadiza Balarabe, El-Rufa’i ya ce yakin basasa lamari ne da Nijeriya ba ta fatan sake ganin irin sa.

Leave a Reply