Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya taya Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti murnar zama sabon Shugaban kungiyar gwamnoni ta Nijeriya.

Buhari ya nuna yakinin cewa kowa ya yi na’am wajen zaben Fayemi, cewa hakan ya nuna tarin karfin gwiwa da takwarorin sa ke da shi a kan sa.

Shugaba Buhari, ya bukaci sabon Shugaban gwamnonin ya dauki zaben sa a matsayin wata dama ta samun kwarin gwiwar yin aiki tare da gwamnatin tarayya, da sauran bangarorin gwamnati.

Buhari ya jadadda cewa, manufar kungiyar gwamnonin ita ce, sanya al’amurran ‘yan Nijeriya sama da komai, tare da kauce wa bambancin akida da siyasa da addini ko kabilanci.

Shugaban Buhari, ya kuma nuna shirin gwamnatin tarayya na tallafa wa kungiyar gwamnonin wajen aiwatar da manufofin ta.

Yayin da ya ke yi wa Fayemi Kayode fatan kammala shugabanci cikin nasara, shugaba Buhari ya yaba wa shugaban kungiyar mai barin gado Abdul’aziz Yari na jihar Zamfara.

Leave a Reply