Kotun sauraren karar zaben Shugaban kasa da ke Abuja, ta yi watsi da karar da jam’iyyar Hope Democratic Party ta shigar, ta na neman a dakatar da mukaddashin Shugaban alkalan Nijeriya mai shari’a Tanko Mohammed daga rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari karo na biyu.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar HDP Ambrose Owuru ne ya shigar da karar a ranar Talatar da ta gabata.

Da ya ke muhawara a kan karar, lauyan Owuru da jam’iyyar HDP Emmanuel Njoku, ya yi korafin cewa a karkashin sashe na 1 (2), da sashe na 6 (6) da sashe na139, da na 239 na kundin tsarin mulkin Nijeriy a na shekara ta 1999, su na so kotun ta hana Buhari gabatar da kan sa ranar 29 ga watan Mayu don karbar rantsuwa a matsayin Shugaban kasa.

Da su ke kafa hujja a kan sashe na 26 (4) da da na 138 (1) na dokar zaben shekara ta 2010, Owuru da HDP sun bukaci kotun ta hana rantsarwar har sai zuwa ranar da za a yi hukunci a kan karar su da ke kalubalantar zaben Shugaban kasa.

Sai dai lauyan shugaba Buhari Wole Olanipekun, da lauyan hukumar zabe Ustaz Usman, da kuma lauyan jam’iyyar APC Akin Olujimi, sun bukaci kotu ta yi watsi da karar saboda rashin ingancin ta.