President Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana dalilin sa na yanke shawarar yin sallar Juma’a a masallacin Juma’ar da ke Fadar shugaban kasa maimakon zuwa babban masallacin Juma’a na Abuja.

Ya ce yana hakane domin kada ya jefa mutane cikin takura a lokacin tawagar sa za ta wuce.

Shugaba Buhari, ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambayar da wakilan limamai daga jihohin da manyan malamai daga dukkanin jihohin Najeriya da birnin tarayya karkashin jagorancin Murshid na babban masallacin Abuja Farfesa Shehu Ahmad Galadanci, ke masa. “

Ya ce Dangane da bukatar da suka nuna ta ya rika zuwa sallar Juma’a a babban masallacin yana so su fahimce cewa, dalili sa na yin sallar Juma’a a masallacin da ke Fadar shugaban kasa, shi ne, saboda kada sanadiyyar zuwa ya takura wa al’umma daga walwala, musamman wadanda ke kan hanyar masallaci da kuma bayan an idar da sallah. “

Ya ce kamar yadda suka sani matukar shugaban kasa zai je wani wuri ana tsananta bincike a kan hanya, wanda kuma hakan zai haifar da cunkoson ababen hawa da na mutane.

Shugaban kasa yana fadin hakan ne a lokacin da malaman suka kai masa ziyarar taya shi murnar samun nasarar sake zama shugaban kasa karo na biyu sakamakon lashe zaben da ya yi.

Ya gode wa malaman bisa gudummowar da suke ba gwamnatin sa ta hanyar yi mata kyawawan addu’o’i, musamman ta fuskar samun dawwamammen zaman lafiya a kasa baki daya.

Leave a Reply