Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce zaben da aka yi a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu, shi ne takara ta biyar da ya yi kuma shi ne na karshe, saboda haka ya na so ya bar abin koyi a bayan sa.

Buhari ya bayyana haka ne, yayin da ya karbi bakuncin zababbun gwamnoni da Sanatocin jam’iyyar APC a wajen liyafar cin abincin dare a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaba Buhari ya sanar da ‘yan majalisun cewa, babu wani abi nda zai iya gudanarwa ba tare da samun goyon bayan su ba.

Ya yi alkawarin yin aiki tare da sabuwar majalisa ta 9, wajen samar da zaman lafiya, da bunkasar arzikin kasa, ya na mai gode wa gwamnoni da sabbin Sanatoci a kan goyon baya da fahimtar da su ka nuna. Shugaban Jam’iyyar ta APC Adams Oshiomhole, ya ce makasudin taron shi ne, domin karfafa hadin kai a tsakanin sabbi da tsofaffin ‘yan majalisar dattawa domin kafa sabuwar dangantaka a tsakanin sashen gwamnati da na majalisar.

Leave a Reply