Rundunar ‘yan Sanda ta Jihar Zamfara, ta ce an yi garkuwa da wani dan kasar Koriya ta Kudu mai suna Jeng Sunail.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ‘yan Sanda ta Jihar Zamfara Mohammed Shehu ya raba wa manema labarai, ya ce ana tunanin an yi garkuwa da mutumin ne a Karamar Hukumar Tsafe.

Sunail, wanda likita ne, wani abokin aikin sa mai suna Li Dong ne ya kai rahoton bacewar sa a Ofishin ‘yan sanda na garin Tsafe.

An dai kai rahoton bacewar Jang Sunail ne, wanda su ka ce ya na zaune ne a wani gida tare da wasu abokan aikin sa su uku.

Shehu, ya ce Kwamishinan ‘yan Sanda na jihar Celestine Okoye, ya tura tawagar jami’an tsaro domin fara bincike da kuma nema da ceto Sunail.

Leave a Reply