Wani bincike da kungiyar kare hakkin jama’a da tabbatar da gaskiya ta SERAP ta gudanar, ya ce rundunar ‘yan Sandan Nijeriya ce kan gaba wajen aikata laifin cin hanci da rashawa.
Kungiyar, ta ce binciken da ta shafe shekaru 5 ta na yi, ya nuna cewa kashi 54 na masu mu’amala da ‘yan sanda su na bada cin hanci, yayin da kashi 63 na ‘yan Nijeriya ke fuskantar kalubalen tambayar su cin hanci duk lokacin da su ka gana da ‘yan Sanda.
Farfesa Akin Oyebode na kungiyar SERAP, ya ce ‘yan siyasa sun zama masu sace dunkiyar kasa wajen inganta yadda ake satar ta.
Kungiyar ta ce wasu bangarori da su ka biyo bayan ‘yan Sanda dangane da aikata laifin karbar cin hanci da rashawa, sun hada bangaren Shari’a, da gudanar da ayyukan gwamnati, da bangaren kula da lafiya da ilimi, da kuma fannin samar da wutar lantarki.
Wani lauya mai zaman kan sa Barista Lawal Ishaq, ya ce rahoton kungiyar SERAP ba abin mamaki ba ne, inda ya ce yadda mutane ke jinjina wa jami’in dan sanda mai gaskiya tare da daukaka darajar sa saboda yin fice daga cikin dubbai, hakan alamace da ke nuna yadda aka samu karancin masu gaskiya tsakanin rundunar.





































