Kungiyar Jama’atul Nasril Islam Reshen Jihar Kaduna, Ta Bukaci Shugabannin Addinin Da Su Yi Amfani Da Matsayin Su Wajen Hada Kan Al’umma A Fadin Jihar.
Sakataren Tsare-Tsare Na Jihar Ibrahim Kufena, Ya Bayyana Hakan A Cikin Wata Sanarwa Da Ya Fitar A Kaduna.
Kungiyar Ta Kuma Bukaci Al’ummomin Gari Da Su Guji Siyasar Ko A Mutu Ko Ayi Rai.
Sannan Ta Shawarci ‘Yan Takara Da Su Ci Gaba Da Yakin Neman Zabe Ta Hanyar Yin Maganganu Da Za Su Inganta Zaman Lafiya A Fadin Jihar.
Sanarwar Ta Kara Da Yin Kira Ga Duk Wadanda Basu Samu Nasara Ba A Zaben Da Su Rungumi Shan Kaye Da Suka Yi Tare Da Taya Duk Wanda Ya Samu Nasara Murna.