Kungiyar Jama’atul Nasril Islam reshen jihar Kaduna, ta bukaci shugabannin addinin da su yi amfani da matsayin su wajen hada kan al’umma a fadin jihar.

Sakataren tsare-tsare na jihar Ibrahim Kufena, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna.

Kungiyar ta kuma bukaci al’ummomin gari da su guji siyasar ko a mutu ko ayi rai.

Sannan ta shawarci ‘yan takara da su ci gaba da yakin neman zabe ta hanyar yin maganganu da za su inganta zaman lafiya a fadin jihar. 

Sanarwar ta kara da yin kira ga duk wadanda basu samu nasara ba a zaben da su rungumi shan kaye da suka yi tare da taya duk wanda ya samu nasara murna.