Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jadadda cewa shi zai yi nasara a zaben da ake gudanarwa a yau Asabar 23 ga watan Fabrairu.
Da manema labarai suka tambayi shugaba Buhari akan ko ko zai mika mulki ga wanda ya yi nasara idan ya fadi zabe, sai ya ce zai taya kan sa murna ne domin shi zan yi nasara.
A safiyar yau Asarar shugaban kasa Muhammadu Buhari da Uwargidar sa Aisha Buhari sun kada kuri’ar su a garin Daura da ke jihar Katsina.
Uwargidan
Shugaban kasa Aisha Buhari ita ta fara kada kuri’ar ta kafin Shugaban kasa
Buhari ya kada ta sa da misalign karfe 8.10 na safiyar yau, kuma sun kada
kuri’ar ne a Kofar Baru, sashin Sarkin Yara A a Daura.