A cigaba da cacar bakin da ake yi tsakanin jami’an sojin Nijeriya da hukumar zabe game da musamman zaben gwamnan jihar Rivers, hukumar zabe ta ce ba ta ce sojojin su je rumfunan zabe ba.

Hukumar zabe ta bayyana haka ne, biyo bayan maganar da jam’iyyar APC ta yi cewa sojojin sun taimaka ne kawai wajen gudanar da sahihin zabe a jihar kamar yadd  a hukumar ta bukata.

Sai dai jami’in hulda da jama’a na hukumar Festus Okoye, ya ce hukumar zabe ba ta ce a kai sojoji ba a rumfunan zaben ba, hasali ma ta ce za ta tattauna da shugabannin rundunar domin ganin sojojin sun tsaya inda ya kamata su tsaya a zabubbukan da za a sake gudanarwa.

Idan dai za a iya tunawa, hukumar zabe ta sanya 23 ga watan Maris a matsayin ranar da za ta gudanar da zagaye na biyu na zaben gwamnonin jahoji shida, sakamakon rashin kammaluwar zaben da aka yi.

Leave a Reply