Duk da ya ke ba a kammala tattara dukkan alkalumman sakamakon zaben gwamnoni da ya gudana a karshen makon da ya gabata ba, ya zuwa yanzu hukumar zabe ta sanar da wasu jahohi.

Wata majiya ta ce yanzu haka manya jam’iyyun siyasar Nijeriya da ‘yan takarar su sun san matsayin su a jahohin da aka kammala sanar da sakamakon su, inda a yanzu haka APC ke kan gaba da jahohi 13, yayin da PDP ke bin ta da jahohi 7.

Daga cikin jahohin da jam’iyyar APC ta samu nasara kuwa akwai Legas, da Gombe, da Kwara, da Kebbi, da Nassarawa, da Yobe, da Neja, da Katsina, da Ogun, da Jigawa, da Kaduna, da Borno da kuma Zamfara. Sai kuma babbar jam’iyyar adawa PDP, wadda ta samu jahohin Abia da Cross Rivers da Delta da Ebonyi da Enugu da Oyo da Akwa Ibom kamar yadda hukumar zabe ta sanar. ement.e[07ʋ1�