Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai kai ziyara a wasu jihohi biyu da ke Kudancin Nijeriya domin mika godiyar sa ta samun nasara a zaben shugaban kasa da ya gabata.

Rahotanni sun ce a ranar Litinin din nan ne, shugaba Buhari zai ziyarci jihohin Akwa Ibom da Imo, domin mika godiyar sa ta samun nasarar lashe zabe da kuma taya ‘yan takarar gwamna jam’iyyar APC yakin neman zabe.

Gabanin zaben gwamnoni da ‘yan majalisun dokoki na jiha da za a gudanar ranar Asabar mai zuwa, shugaba Muhammadu Buhari zai kuma ziyarci jihohin Kaduna da Taraba da Sokoto da kuma Katsina.

Sai dai har yanzu babu wani tabbaci game da abubuwan da shugaba Buhari zai aiwatar yayin ziyarar, amma wani binciken manema labarai ya tabbatar da cewa, shugaba Buhari zai gudanar da zaman sauraren ra’ayoyi domin mika godiyar sa ta samun nasara.