Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce ta na kalabulantar hukuncin da kotu ta yanke na hana ta cigaba da tattara sakamakon zaben gwamna a jihar Bauchi.

INEC ta garzaya kotu ne bayan da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada umarnin cewa, a dakatar da tattara sakamakon zaben gwamna na yankin Tafawa-Balewa da ke jihar Bauchi da aka gudanar makonni 2 da su ka gabata.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kai na hukumar INEC Festus Okoye ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya kara da cewa, sun daukaka karar ne domin a kyale hukumar ta cigaba da tattara kuri’un zaben jihar.

Okoye ya ce su na kalubalantar wannan mataki da kotu ta dauka ba tare da hurumin ta ba, sanna ta ce duk da an dakatar da tattara kuri’un zaben gwamna za a cigaba da aiki a kan zaben majalisar dokokin na yankin Tafawa Balewa.

Yanzu dai hukumar INEC ta ce ta yi wa umarnin kotun biyayya amma za ta maka ta karar a gaban kuliya domin a rushe hukuncin da Alkali Inyang Ekwo ya yanke bayan gwamna Muhammad Abubakar ya shigar da kara.