Dan kakarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da uwargidan sa Titi Abubakar sun kada kuri’ar su  yola a cigaba da gudanar da zabe shugaban kasa da ake gudanar a yau asabar 23 ga watan fabrairu.

Da manema labarai suka tambaye shi a kan yadda zaben ke gudana, ya yi matukar nuna farin cikin sa a kan yadda mutane suka fito domin nemama kan su ‘yanci ta hanyar zaben wanda su ke so.

Atiku Abukakar ya ce zai karbi sakamakon zabe koda bai yi nasara ba domin ya yadda da zarin dimokradiyya.

A karshe ya yi wa ‘yan Nijeriya fatan alheri da kuma addu’ar yin zabe lami lafiya ba tare da samun wani hargitsi ba.