Jam’iyyar PDP ta lashe zaben kananan hukumomi 2 daga cikin ukun da su ka rage ba a kammala ba a birnin tarayya Abuja, yayin da jam’iyyar APC ta samu kujera daya.

A mazabar Kuje, baturen zaben Farfesa Titus Ibekwe, ya bayyana Abdullahi Sabo na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya yi nasara da kuri’u 19,090, yayin da Abdullahi Galadima na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 15,187.

A mazabar Bwari kuwa, Baturen zaben Farfesa Mohammed Umaru, ya bayyana Gabaya na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 31,114, yayin da Musa Dikko na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 24,137.

A mazabar Kwali kuma Baturen zaben Farfesa Simon Kawe, ya bayyana Chiya na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 14,245, yayin da Ibrahim Daniel na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 14,189.

Yanzu haka dai jam’iyyar APC na da kujeru hudu daga cikin shida na kananan hukumomin birnin tarayya Abuja, yayin da jam’iyyar PDP ta samu biyu.