Sanatoci 64 da kuma ‘yan majalisar wakilai su 151 ne ba za su dawo majalisar kasa a karo na 9 cikin watan Yunin wannan shekarar ba.

Sanatoci 45 da ‘yan majalisar wakilai kimain su 209 kacal suka iya tsallake siradin zabukan da aka gudanar a ranar Asabar idan aka yi la’akari da sakamakon zaben da Hulkumar INEC ta fitar.

Sababbin da aka zaba su 15 tsofaffin gwamnoni ne a jihohin su, 42 kuma daga cikin sanatoci 64 na sanatocin da basu dawo kan madafun ikon su ba sun gaza cin zabe a cikin watan Okotobar shekarar da ta gabata a lokacin zaben fid da gwani na jam’iyyun su.

Sauran 22 sun sha kaye ne a zabukan da aka gudanar a ranar Asabar.

Jam’iyyar APC mai mulki tana da sanatoci 64 da aka zaba a lokacin zaben na ranar Asabar, inda PDP take da 41 sai kuma jam’iyyar YPP tana da sanata daya.