Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zabe Na Kasa, INEC
Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zabe Na Kasa, INEC

Rahotanni na cewa, akwai yiwuwar jam’iyyau goma ne kacal za su samu tsira wajen ci-gaba da fafatawa ta fuskar gudanar da harkokin siyasa a fadin kasar nan.

Wata majiya ta ruwaito cewa, akwai yiwuwar hukumar zabe ta kasa za ta kwace rajistar kimanin jam’iyyun siyasa 81 sakamakon rashin cika sharudda.

Bisa kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekara na 1999 sashe na 225, zai tursasa wa hukumar zabe kwace rajistar wasu jam’iyyu sakamakon rashin cika sharudda da kuma tanadin tsare-tsare.

Daga cikin sharuddan da kowace jam’iyya za ta cika kuwa sun hada da tabbatar da cika sharuddan samun rajista daga hukumar zabe, sannan kowace jam’iyya ta samu kaso 25 cikin 100 na adadin kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasa ko da a jiha guda.

An kuma so kowace jam’iyya ta samu makamancin wannan kaso a cikin karamar hukuma daya yayin zaben kujerar gwamna.

Binciken manema labarai ya tabbatar da cewa, baya ga jam’iyyun APC da PDP, sauran jam’iyyun da za su samu tsira bisa ga tsari doka sun hada da APGA da YPP da AA da APM da SDP da kuma PRP.