Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci wani taro da shugabannin rundunonin tsaron Nijeriya wanda ya gudana a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya Muhammad Adamu ya sanar da haka ga manema labarai a karshen zaman tattaunawar.

Wadanda su ka halarci taron sun da babban Hafsan tsaron Nijeriya  Janar Gabriel Olonisakin,da Shugaban rundunar sojin kasa Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai da shugaban Rundunar Sojan Ruwa Riya Admiral Ibok Ekwe Ibas, da shugaban Rundunar Sojan Sama,Iya Mashal Abubakar Sadibue.

Sauran sun hada da Darakta Janar na Hukumar tsaro ta farin kaya DSS Yusuf Bichi, da mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro Babagana Monguno da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da Ministan tsaro Mansur Dan- Ali da daraktan Hukumar tattara bayanan sirri na kasa Malam Ahmed Abubakar.