Babban hafsin sojin sama na Najeriya Air Marshal Sadique Abubakar ya umurci manyan kwamandojin rundunar da suka hada da wadanda ke aiki a fagen daga da su tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin al’ummar wuraren da suke aiki a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da za a gudanar a wannan makon.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun jami’in yada labarai da hulda da jama’a na rundunar AIR Commodore Ibikunle Daramola a Abuja.

Sadique ya kuma bada umurnin turawa da kayayyakin aikin rundunar da kuma masu binciken kwakwaf da jiragen da za su rika shawagi zuwa sassa daban-daban gabannin zaben.

Ya ce an kara da turawa da wasu jami’an tsaro domin taimakawa jami’an ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro zuwa wuraren da ake ganin akwai yiwuwar samun hatsaniya.

Daramola ya ce babban aikin kwamandojin rundunar shine tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma, kuma rundunar ba za ta aminta da kasa cika wannan aiki ba.