Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, za ta gudanar da zabe a yankunan da ba a gudanar da zabe ba a ranar Asabar, 23 ga watan Farairu.

Zaben dai zai gudana ne a ranar 9 ga watan Maris, tare da na gwamnoni da na majalisun jiha da kuma na birnin tarayya Abuja.

Hukumar zaben ta kuma umurci kwamishinonin zabe na jiha su gabatar wa mata da rahoto a kan rikice-rikicen da su ka afku domin daukar matakin da ya kamata.

An kai wannan matsaya ne, yayin ganawar da aka ta gudana tsakanin manyan jami’an hukumar zabe da kwamishinonin zabe na jihohi 26 da birnin tarayya Abuja.

Leave a Reply