Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zabe, INEC
Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zabe, INEC

Shugaban Hukumar zabe mai ta kasa Farfesa Mahmood Yakubu ya ce da misalign karfe 6:00 na yammacin yau za ne aka bude cibiyoyin karbar sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya a babbar shelkwatar hukumar da ke Abuja.

Farfasa Yakubu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a a Abuja, sannan ya ce mutune 73, 000 ne masu sa-ido a harkokin zabe za su lura da yadda zaben ke gudana a fadin Nijeriya.

Ya kara da cewa, miliyoyin  ‘yan Nijeriya za su zabi wanda zai shugabnci su na tsawon shekaru hudu masu zuwa, tare da ‘yan majalisar wakilai da na dattawa.

Inda dai za iya tunawa, Hukumar zabe ta shirya gudanar da wannan zabe a rarar Asabar din da ta gabata, ammam wasu dalilai masu karfi suka sa dole ta dage zuwa yau asabar 23 ga watan  fabrairu. wanda kawo yanzu ‘yan Nijeriya na ci gaba da gudanar da zaben su kamar yadda aka tsara.

Mukaddashin Babban Sifeton ‘yan sanda ya tabbatarwa da ‘yan Nijeriya cewa, sun tanaji ‘yan sandan da za su kula da wannan zabe, cikin ikon Allah zai gudana lami lafiya.