Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya gabbatar da wasu sharudda biyar da ya ke son Shugaba Muhammadu Buhari ya cika, yayin wani taro da kwamitin zaman lafiya a karkashin jagorancin Abdulsalami Abubakar.

Sharuddan kuwa sun hada da bude asusun bankunan ‘yan jam’iyyar adawa da aka rufe, da janye sojoji daga wuraren zabubbukan da za a yi nan gaba, a kuma rika tantance masu zabe kafin a fara kada kuri’u a sauran zabubbukan da su ka yi saura, sannan a saki duk ‘yan siyasar da ake tsare da su ba bisa ka’ida ba.

Haka kuma, Atiku ya bukaci hukumar zabe ta bude shafin yanar gizo, ta yadda duk jam’iyyun siyasar da ke takara za su iya shiga su duba yadda abubuwa ke gudana.

Ana sa ran kwamitin zaman lafiyar zai gana da Shugaba Muhammadu Buhari domin gabatar masa da wadannan sharudda da Atiku Abubakar ya gindaya.