FG To Inaugurate National Plan For Financing Safe Schools In September

Majalisar Wakilai ta umarci Ministar kudi Zainab Ahmed ta gaggauta bayyana a gaban ta, domin gabatar da adadin kuɗaɗen da aka biya da sunan tallafin man fetur.

Shugaban Kwamitin Binciken Kuɗaɗen man Fetur na majalisar wakilai Aliyu Musa ya bada umarnin, lokacin da Daraktan kudi na Cikin Gida a Ma’aikatar kudi ya bayyana a gaban kwamitin.

Tun farko dai Kwamitin ya bada wa’adin zuwa ranar 16 Ga watan Agusta a kai ma shi kwafen bayanan da su ka haɗa da Jimla da adadin kuɗaɗen da aka kwasa daga Asusun Haɗaka na tara kuɗaɗen haraji aka biya tallafin man fetur da su, tun daga shekara ta 2013 zuwa 2022.

Kwamitin, ya kuma nemi a kai ma shi dukkan kwafen takardun biyan kuɗaɗen da aka ce an yi, sannan ya nemi a kai ma shi sunayen kamfanonin da aka taɓa biya kuɗaɗen tallafin man fetur da adadin da aka riƙa biyan kowanne.

Aliyu Musa, ya ce dole Ministar ta bayyana a gaban su domin gabatar da bayanai masu damun ‘yan Nijeriya, ciki kuwa har da shirin da gwamnati ke yi na ciwo bashi a biya tallafin man fetur.