Biyo bayan dambarwar da aka samu yayin da ake tattara alkalumman sakamakon zaben gwamnan jihar Kano, masana al’amuran siyasa sun jinjina wa kwamishinan ‘yan sanda na jihar Muhammad Wakili a kan rawar da rundunar sa ta taka.

Masanan sun ce ba kamar yadda aka saba samun hadin bakin takanin ‘yan sanda da ‘yan siyasa da sauran jami’an tsaro da hukumar zabe wajen shirya magudin zabe ko aringizon kuri’u ba, kwamishina Muhammad Wakili ya sha bambam da sauran jami’ai.

Sun ce ganin yadda ‘yan sanda su ka kama mataimakin gwamnan da kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo, za a san da gaske ‘yan sandan ba wasa su ka fito ba. Idan dai za a iya tunawa, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, wanda aka fi sani da lakabin ‘Maza-kwaya Mata-kwaya’, ya yi alkawarin aiki tsakanin sa da Allah ba zai bari wani dan siyasa ya yaudare shi da kudi ba