Wasu ‘yan bindiga sun kai mummunan hari a kauyen Kawaye da ke cikin karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara, inda su ka kashe mutane goma sha uku a ranar Talatar da ta gabata.
Wani mazaunin kauyen da ya tsallake rijiya da baya Aliyu Muhammad, ya ce ‘yan bindigar sun shiga kauyen ne a kan babura da yawa tare da bude wa jama’a wuta.
Ya ce yayin da su ka sauka daga kan baburan su, sai su ka fara banka wa motoci da Babura da kekuna da shaguna da sauran gidajen jama’a wuta, sannan su ka yi awon gaba da hakimin yankin da matar sa da wasu mutane arba’in.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar SP Muhammad Shehu ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya tabbatar da mutuwar mutane goma sha daya sanadiyyar harin.
Kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa, rundunar ta tura jami’an ta da ke aiki tare da dakarun Soji zuwa dazuzzukan yankin domin ceto hakimin da matar sa da sauran mutanen da ‘yan bindigar su ka yi garkuwa da su.
Rundunar ‘yan sandan, ta kuma sha alwashin kama ‘yan bindigan tare da duk masu daukan nauyin su.