Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa, wasu ‘yan bindiga sun afka ma wani kauye, inda su ka kashe mutane da dama a karamar hukumar Shinkafi.

An dai kai harin ne a kauyen Kware a tsakiyar daren Lahadin da ta gabata, sannan baya ga kashe mutanen, ‘yan bindigar sun kuma kone gidajen mutane da dama kamar yadda wani mazauni kauyen ya ce shi ma an kone gidan sa.

Ya ce sun kirga gawawwakin mutane kimanin 40 da ‘yan bindigar su ka kashe, yayin da mutanen kauyen da dama sun yi gudun hijira zuwa makwafta.

Sai dai ya zuwa yanzu rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara ba ta fitar da sanarwa game da al’amarin ba.