Wani dan majalisa mai wakiltar mazabar Pengana a jihar Kwara Mista Ezekiel Afon, ya mutu sa’o’i kadan bayan ya yi nasarar lashe zabe a mazabar sa.

Sakataren jam’iyyar APC na jihar Bashir Sati ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a birnin Jos na jihar Fialato, inda ya ce Afon ya mutu ne a yammacin ranar Lahadin da ta gabata, bayan ‘yar gajeruwar rashin lafiya.

Ya ce abin bakin ciki ne cewa sun rasa Afon, daya daga cikin jajirtattun ‘yan jam’iyyar kuma jajirtaccen dan majalisa, bayan an kaddamar da shi a matsayin wanda ya sake lashe zaben kujerar sa.

Bashir Sati ya cigaba da cewa, duk da yak e sun san bas hi da lafiya na dan wani lokaci, amma labarin mutuwar sa ya jefa su cikin juyayi.

An dai fara zaben Afon a majalisar dokoki a karkashin jam’iyyar PDP a shekara ta 2015, amma ya sauya sheka zuwa APC a shekara ta 2017.