Abba Kabir Yusuf, Dan Takarar Gammna A jihar Kano A jam’iyyar PDP
Abba Kabir Yusuf, Dan Takarar Gammna A jihar Kano A jam’iyyar PDP

Rahotanni na cewa, yanzu haka za a fafata da dan takarar jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf a zaben gwamnoni da na majalisar dokoki da za a yi ranar Asabar mai zuwa a jihar Kano.

A wani hukunci da kotun daukaka kara ta yanke, ta dakatar da hukuncin da kotun farko ta yanke na umartar hukumar zabe ta kasa ta cire sunan Abba Kabir daga jerin ‘yan takarar da za su fafata a zaben neman kujerar gwamnan jihar Kano.

A ranar Litinin da ta gabata ne, mai shari’a Lewis Allagoa na babbar kotun tarayya da ke Kano ta yanke hukuncin a hana PDP shiga zaben saboda ba ta gudanar da zaben fidda ‘yan takara a kan ka’ida ba.

Daya daga cikin wadanda su ka nemi jam’iyyar PDP ta tsaida su takarar gwamna a jihar Kano Ali Amin-Little ne ya shigar da karar, ya na kalubalantar matakin tsaida Abba a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP.