Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce wa’adin mulkinsa na biyu zai fi tsauri fiye da na farko.

Buhari, ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin ‘yan majalisar ministocin sa da suka kai masa ziyara a fadar gwamnati a birnin Abuja domin taya shi murnar sake lashe kujerar shugabancin kasa a wa’adi na biyu.

Ya ce yana ganin wa’adin sa na shekaru hudun karshe, zai fi tsauri kan marasa kishin kasa, wannan ne ya sa a lokacin yakin neman zabe, ya yi magana akan manyan manufofin gwamnatin sa.

Shugaba Buhari, ya ce, bai yi kasa a gwiwa ba wajen tunatar da al’ummar Najeriya game da alkawuran sa na tabbatar da tsaro da bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma samar da ayyuka ga matasa har ma da yaki da cin hanci da rashawa.