Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC Ibrahim Magu, ya bukaci a kirkiro sabbin dokoki masu tsauri a kan masu satar mai.

Mai magana da yawun hukumar EFCC Tony Orilade ya bayana haka a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, biyo bayan ziyarar da shugaban hukumar ya kai wa kwamandan sojojin ruwa Kwamanda S. Bura a garin Fatakwal na jihar Rivers.

Sanarwar ta ta kara da cewa, Ibrahim Magu ya samu wakilcin shugaban hukumar na yankin kudu maso kudancin Nijeriya Abdulrasheed Bawa.

Abdurasheed Bawa ya ce, yankin kudancin Nijeriya har yanzu ya na cikin muhimman shiyyoyi a kasar nan, musamman ganin cewa daga nan ne ake hako mafi yawan man da Nijeriya ke saidawa domin samun kudin shiga.x

Leave a Reply