A yau ne hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ke gudanar da karashen zaben Gwamna a mazabun wasu jihohi, in da gwamnonin da ke kan karaga ke fafatawa da abokan hamayyar su da ke neman kawar da su daga madafun iko.

Jihohin da ake gudanar da karashen zaben sun hada da Kano, da Sokoto, da Filato, da Benue, da kuma Bauchi,  bayan Hukumar ta INEC ta bayyana zaben jihohin a matsayin wadanda ba su kammala ba tun a ranar 9 ga wannan wata na Maris.

Kodayake INEC ta ce, za ta gudanar da karashen zaben a jihohi 18, amma hankula sun fi karkata a wadannan jihohin da aka lissafa, yayin da kotu ta bayar da umarnin dakatar da zaben a jihar Adamawa

Jam’iyyar APC na fatan karbe kujerun gwamnonin jihohin Sokoto da Benue, yayin da PDP ke kokarin ganin ta karbe Kano da Filato da kuma Bauchi.

Wadannan jihohin na da matukar muhimmanci a siyasar Najeriya saboda yawan al’ummar su da kuma kuri’un da suke bayarwa, abinda ya sa jam’iyyun ke fatan lashe su.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci al’ummar mazabun da ake gudanar da zaben da su fito kwan su da kwarkwatar su domin kada kuri’ a.

Leave a Reply