Jam’iyyar APC a jihar Imo, ta zargi gwamna Rochas Okorocha da yin amfani da wasu jami’an tsaro wajen murde sakamakon zaben gwamna da aka yi ranar Asabar da ta gabata.

APC ta yi kira ga magoya bayan ta su saka ido a kan kuri’un da su ka jefa, domin ganin cewa Rochas bai samu damar murde sakamakon zabe domin surukin sa ya zama gwamna ba.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Cif Marcelinus Nlemigbo ya bayyana haka, yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai.

Nlemigbo, ya yi kira ga hukumar soji da rundunar ‘yan sanda su tsawata wa jami’an su don kada a yi amfani da su wajen aikata magudin zabe.

Rochas dai ya na daga cikin gwamnonin jam’iyyar APC da su ka ci zaben kujerun majalisar dattawa, bayan karewar wa’adin sa na biyu a kujerar gwamna. et=|07�1