Rundunar Sojin Najeriya Ta Kaddamar Da Bincike Kan Zargin Saba Dokokin Aiki Da Kuma Rashin Nuna Kwarewa Kan Wasu Jami’anta Da Suka Yi Aiki A Zaben Shugaban Kasa Da Na ‘Yan Majalisun Tarayya.
Babban Hafsin Sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai, Ya Bayyana Haka A Wajen Taron Kwamandojin Rundunar Wanda Ya Gudana A Shelkwatar Rundunar Dake Abuja.
Ya Ce Gwamnonin Jihohin Bayelsa, Oyo, Da Ogun Sun Shigar Da Koke-Koke Tare Da Neman A Hukunta Wasu Jami’an Soji Da Suka Yi Aiki A Jihohinsu.
Sai Dai Buratai Bai Ce Uffan Ba Akan Jihar Rivers Wacce Ake Gani An Samu Rikice-Rikice Da Dama A Lokacin Zabubbukan Da Suka Gabata.
Sannan Ya Ja Hankali Kan Wasu ‘Yan Siyasa Dake Shirya Makarkashiyan Tada Hatsaniya A Lokacin Zaben Gwamnoni Da Na ‘Yan Majalisun Jihohi Da Zai Gudana A Wannan Makon.
Ya Kuma Kara Jaddada Cewa Rundunar Za Ta Binciko Tare Da Hukunta Duk Mutanen Da Ke Da Hannu A Kisan Da Aka Yiwa Jami’an Soji A Lokacin Zabubbukan.