Rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da bincike kan zargin saba dokokin aiki da kuma rashin nuna kwarewa kan wasu jami’anta da suka yi aiki a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.
Babban hafsin sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai, ya bayyana haka a wajen taron kwamandojin rundunar wanda ya gudana a shelkwatar rundunar dake Abuja.
Ya ce gwamnonin jihohin Bayelsa, Oyo, da Ogun sun shigar da koke-koke tare da neman a hukunta wasu jami’an soji da suka yi aiki a jihohinsu.
Sai dai Buratai bai ce uffan ba akan jihar Rivers wacce ake gani an samu rikice-rikice da dama a lokacin zabubbukan da suka gabata.
Sannan ya ja hankali kan wasu ‘yan siyasa dake shirya makarkashiyan tada hatsaniya a lokacin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da zai gudana a wannan makon.
Ya kuma kara jaddada cewa rundunar za ta binciko tare da hukunta duk mutanen da ke da hannu a kisan da aka yiwa jami’an soji a lokacin zabubbukan.