Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gargadi ‘yan jarida game da illolin da yada rahotannin bogi da shaci-fadi ke haifarwa.

Buhari ya gargadi ‘yan jarida, su daina bari wasu miyagun mutane su na rinjayar su wajen yada rahotanni masu cin karo da akidun zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umma.

Shugaba Buhari ya yi gargadin ne, yayin da ya karbi bakuncin kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya NUJ, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Buhari ya bukaci a kawo karshe, tare da dakile yawaitar  rahotannin bogi a fadin Nijeriya, wadanda ke haifar da barazana ga zaman lafiya da kuma haddasa nakasu a bangaren ci-gaban kasa ta kowace fuska.

Kiran dai ya na da mahimmanci a daidai wannan lokaci kamar yadda shugaban ya bayyana, sakamakon yadda rayuka da dama su ka salwanta baya ga asarar tarin dukiya sanadiyar yaduwar rahotannin bogi.