Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna, ta bukaci matasa su guji yin ganganci ko wauta da sunan murnar shugaba Buhari ya ci zabe.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Yakubu Sabo ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kaduna.

Ya ce kiran ya zama wajibi, ganin yadda mutane su ke tukin saida rai a titunan Kaduna domin murnar nasarar da Buhari ya samu a zabe.

Yakubu Sabo ya cigaba da cewa, za su kama duk wanda su ka gani ya na tukin gaganci da sunan murnar nasarar cin zabe a titunan Kaduna.

Ya ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar Ahmad Abdurrahman, ya yi kira ga iyaye da masu unguwanni su rika ja wa matasa kunne game da yin hakan.

A karshe ya ce rundunar ‘yan sanda za ta cigaba da hada hannu da sauran jami’an tsaro a jihar Kaduna domin samar da tsaro.

Leave a Reply