Rahotanni daga Mali sun ce adadin Fulani makiyaya da wasu mahara suka hallaka ya karu daga 60 zuwa sama da mutum 100.

Tun da fari dai, magajin garin Bankass da ke tsakiyar yankin Mali, Moulaye Guindo, ne ya soma bayyana rahoton harin kan Fulanin makiyaya a kauyen Ogossogou-Puel.

Adadin mamatan ya karu ne zuwa 115, bayan da hadin gwiwar jami’an tsaro da sauran jama’ar kauyen suka kammala tantance wadanda harin ya rutsa da su, inda aka gano gawarwakin mutanen da suka bace.

‘Yan bindigar da ake kyautata zaton cewa maharba ne daga kabilar Donzo, sun kai mummunan farmakin ne da misalin karfe 4 na asubahin yau Asabar.

Yankin Tsakiya Mali a baya bayan nan ya yi kaurin suna wajen fuskantar matsalolin tsaro da suka hada da hare-haren mayaka masu da’awar Jihadi da kuma rikicin kabilanci tsakanin kabilun Dogon, Bambara da kuma Fulani.

Ko a watan Maris na shekarar 2018, dubban Fulani ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Bamako na kasar Mali, domin nuna bacin ransu dangane da yadda ake kai wa kabilar hare-hare bisa zargin cewa ‘yan ta’adda ne.