Abdul-Aziz Yari, Former Governor Of Zamfara Sate
Abdul-Aziz Yari, Former Governor Of Zamfara Sate

Gwamnan jihar Zamfara Abdul-Aziz Yari, ya ce sai gwamnatocin jihohin da ke makwaftaka da jihar sa sun hada gwiwa kafin a samu nasarar fatattakar ‘yan bindigar da ke addabar al’ummar yankin.

Abdul-Aziz Yari ya bayyana hakan ne, a lokacin wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta BBC a Abuja, inda ya ce akwai bukatar a ba sojoji manyan bindigogi domin yaki da maharan da ke yankin.

Ya ce sojojin Nijeriya su na da horo da kayan aiki, sannan su na da cikakken iko.

Yari ya cigaba da cewa, ya kamata sojoji su nuna wa wadannan maharan ba sani ba sabo wajen yaki da su.
3