Kungiyar Kwallon kafa ta Paris St-Germain ta yi ban kwana da gasar cin kofin zakarun turai Champions League ta bana, bayan da ta yi rashin nasara a hannun Manchester United da ci 3-1 a gida.
United ce ta fara cin kwallo ta hannun dan wasan ta Romelu Lukaku minti biyu da fara wasan, sai dai dan karamin lokaci PSG ta rama ta hannun dan wasan ta Juan Bernat.
Ana tsaka da wasa ne United ta kara kwallo ta hannun Marcus Rashford inda Buffon ya kasa rike wa, nan take Romelu Lukaku ya jefa a raga.
Daga baya ne United ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida, kuma Marcus Rashford ya buga ya ci, sai dai fenariti ya jawo cecekuce bayan da alkalin wasa ya je yaga abin da ya faru a na’urar da take taimaka masa yanke hukunci.
A wasan farko da suka fafata a Old Trafford a watan Febrairu, PSG ce ta yi nasara da ci 2 nema, amma cin kwallo uku da United ta yi a Faransa ya ba ta damar kai wa zagaye na gaba.