Olusegun Obasanjo, Tsohon Shugaban Kasa
Olusegun Obasanjo, Tsohon Shugaban Kasa

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya yi tir da wadanda ke adawa da yunkurin Atiku Abubakar na zuwa kotu domin ya kalubalanci nasarar da shugaba Buhari ya samu a zaben shekara ta 2019.

Obasanjo ya ce, masu neman Atiku ya hakura da zuwa kotu ba mutanen kirki ne ba, ya na mai cewa su na neman kawo tashin hankali ne a Nijeriya.

Tsohon shugaban kasar ya kuma yi tsokaci game da zaben jihar Osun da kotu ta rusa, inda ta ce dan takarar jam’iyyar PDP Sanata Ademola Adeleke ne ainihin wanda ya lashe zaben.

Obasanjo, ya ce abu ne mai kyau a ce Atiku Abubakar ya garzaya gaban Alkalai domin a fitar masa da hakkin sa.

Ya ce Nahiyar Afrika da ma Duniya baki daya ta na kallon zaben da ake yi a Nijeriya, ya na mai yaba wa matakin da Ademola Adeleke ya dauka har ya samu nasara a kotu bayan da farko an ce ya fadi zabe.