Jam’iyyun adawa a jihar Zamfara, sun ce idan hukumar zaben ta kasa ba ta rushe zaben da ya gudana a makon da ya wuce na Shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da ke cike da magudi, lalllai a kwai matsala.
Shugaban hadakar jam’iyyun adawa, kuma dan takarar gwamna a jam’iyyar Apga Sani Abdullahi Wamban Shinkafi, ya tabbatar da haka a dakin taron wakilai kafafen yada labarai da ke Fadama a Gusau Baban birnin jihar Zamfara.
Shugaban hadakar ya yi zargin cewa suna da tabbacin tun a ranar jajiberin zaben ne aka shirya wannan makircin yin magudi a hedikwatar ‘yan sanda da ke jihar.
Ya ce a kan huka suke kira ga Sufeto janar na ‘yan sand da ya gaggauta dauke Kwamishinan sa daga jihar Zamfara, ita kuma Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta kori Kwamishinar zaben jihar don ba ta cancanci wannan aikin ba.
Wamban Shinkafin a madadin Shugaban jam’iyyun adawa sun dau alwashi bin umarni da Shugaban kasa ya bada na ganin bayan duk wanda ya saci akwati ko ya nemi kawo magudin zabe a jihar Zamfara, a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha mai zuwa.
Gamayyar jam’iyyun sun hada da Jam’iyyar PDP, da Apga, da NRM , da ADC, da YPP , da ACCORD, da ABP, da sauransu.